GABATARWA
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINkAI
Tsira da Amincin Allah sun tabbata ga fiyayyen Halitta Annabi Muhammadu (Sallallahu alaihi wa sallam) tare da mutanen gidanSa da sahabbanSa.
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINkAI
Tsira da Amincin Allah sun tabbata ga fiyayyen Halitta Annabi Muhammadu (Sallallahu alaihi wa sallam) tare da mutanen gidanSa da sahabbanSa.
((In da za ku qirga ni‟imomin Allah, to ba za su qirgu ba)).
Allah (Subhanahu wa ta'ala) ya yi mana babbar ni‟ima a wannan qarnin, ta bayyanar wani babban bawan Allah a cikinmu, wanda zuwansa ya zama mana fitilar da take haskaka mana mafuskantarmu.
Ya zama sinadarin tsarin rayuwarmu, wanda ya sa muka rarrabe tsakanin qarya da gaskiya, muka gane gaskiya komin lulluvewar da aka yi mata, muka kuma gane qarya komin kwalliyar da aka yi mata.
Shi ne wanda ya rayata yin aiki da Alqur‟ani, da kuma sashi jagora a cikin dukkan al‟amurranmu, ya kuma nuna haqiqanin aiki da sunnah ba tare da cika-baki ba. Sannan ya nuna mana yanda ake aiki da shari‟a tare da yi mata kwalliya da haqiqa, wanda kullum tunaninsa shi ne tsamo al‟ummar Annabi Muhammadu (Sallallahu alaihi wa sallam) daga dukkan halaka da karkacewa.
Aikinsa dare da rana shi ne qoqarin kusantar da su ga Allah, ta hanyar da ta zamo ingattacciya, miqaqqiya, kuma bayyananniya.
Wato shaihinmu, jagoranmu, shugabanmu, farin-cikin rayuwarmu, hasken idanunmu, Ash- Shaikh Ash-Shareef Ibraheem Saleh Al-Husainy (Radiyallahu Anhu). Daga cikin ayyukan da Shaihu ya yi mana shi ne rubuta wannan littafi mai tarin albarka, wanda da ace duk mutanen duniya za su yi aiki da shi, to da duk an huta da maganar tashin hankali da zargin juna.
Domin a cikinsa ya nuna mana haqqin kowa akan kowa, haqqin ubangiji akan bayinsa da tunatar da su baiwa da xaukakar da ya yi musu, haqqin iyaye akan „ya‟yansu, da na „ya‟ya akan iyayensu, haqqin malamai akan almajiransu, da na almajirai akan malamansu, da na „yan uwa a tsakaninsu, haqqin uban gida akan yaronsa, da na yaro akan uban gidansa, da kuma haqqin shuwagabanni akan mabiyansu, da na mabiya akan shuwagabanninsu. Kuma duk yana yin magana ne da Alqur‟ani da Hadisin Annabi (Sallallahu alaihi wa sallam).
Sannan ya bayyana mana waye muqaddami kuma waye muridi, ya kuma nuna mana nauyin da ya rataya akan kowannensu. Sannan ya gyara mana kurakuren da ake yi a wajen gabatar da ayyukan xarikar Tijaniyya, ya kuma bayyana mana hukunce-hukunce da sharuxxanta, tun daga na inganci har zuwa na cika.
Ya bayyana mana haqiqanin sufanci tare da asalinsa a cikin Alqur‟ani da Sunnah, ya fitar da shi (sufanci) daga lungun da aka tura shi, wanda har ya sa ake shan fama wajen fahimtar zantukan masu tasuwuf.
Kai a jimillance dai, wannan littafi bai bar wani abu da ya kamata a sani ba, wanda ya shafi addini da rayuwa, sai da ya faxe shi, kuma cikin salo mai sauqin fahimta da saurin kiyayewa. Allah ya saka ma Maulana da alkhairi. Wannan littafi shi ne “An- nahajul Hameed fi ma yajibu alal muqaddami wal murid”. Wato “Kyakkyawar Hanyar sanin abin da ya wajaba akan muqaddami da muridi”.
Wannan littafi na "Nahajul Hameed….", maulana Sharif ya yi shi ne tun shekaru da yawa da suka wuce. An buga shi ba sau xaya ba a qasashe da dama na duniya, saboda muhimmancinsa da tarin amfaninsa, har ga shi yanzu Allah ya sa an samu wani xan uwa daga cikin masoyan maulana ya yi yunquri ya fassara shi daga Larabci zuwa Hausa; domin masu sha‟awar karatun Hausa su ma su amfana da lu‟alu‟an dake cikin littafin. Wannan xan uwa namu shi ne Malam Salihu Abubakar Qaura. Babu shakka wannan xan uwa ya yi qoqari qwarai da gaske, domin kuwa ya kiyaye ma‟anar lafuzzan da Shaihu ya faxa, da kuma ba kowane lafazi ma‟ana mafi kusanci, da kauce ma tsawaita bayani wanda mafi yawancin masu fassara suke yi, har su fita daga ainihin manufar littafin. Malam Salihu Qaura, Allah ya saka masa da alkhairi.
A qarshe, muna roqon Allah ya tsawaita mana rayuwar Maulana, ya kuma qara masa lafiya, domin mu ci gaba da tsotsa daga abin da aka saba ba mu muna sha. Allah kuma ya sa a samu wasu waxanda za su yi qoqarin fassara wasu daga littattafan maulana da sauran harsuna, domin dukkan littattafansa sun cancanci a yi musu hakan. Shi kuma Malam Salihu Qaura, Allah ya sa wannan ya zama matakin farko na ci gaban irin waxannan aiyuka masu amfani ga al‟ummah.
Wassalamu Alaikum.
Muneer Ja‟afar
Katsina. NIGERIA.
22/05/2012
No comments:
Post a Comment
YI MANA QARIN BAYANI KO GYARAN KUSKURE