Pages

20 Sept 2016

GABATARWA (KYAKKYAWAR HANYAR SANIN WAJIBIN MUQADDAMI DA MURIDI)

KARATUN LITTAFIN "KYAKKYAWAR HANYAR SANIN WAJIBIN MUQADDAMI DA MURIDI" na SHEIKH SHARIF IBRAHIM SALEH AL-HUSAINI (CON) Shugaban Kwamitin Bayar da Fatawa Karkashin Majalisar Koli ta Addinin Musulunci A Tarayyar Najeriya.

GABATARWA DAGA SHEIK MUNEER SHEIKH JA'AFAR KATSINA

DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI Tsira da Amincin Allah sun tabbata ga fiyayyen Halitta ANNABI MUHAMMADU (SALLALLAHU ALAIHI WA SALLAM) tare da mutanen gidanSa da sahabbanSa.

(In da za ku qirga ni'imomin ALLAH S.W.T  to ba za su qirgu ba), ALLAH (Subhanahu wa ta'ala) ya yi mana babbar ni'ima a wannan qarnin, ta bayyanar wani babban bawan Allah a cikinmu, wanda zuwansa ya zama mana fitilar da take haskaka mana mafuskantarmu, Ya zama sinadarin tsarin rayuwarmu, wanda ya sa muka rarrabe tsakanin qarya da gaskiya, muka gane gaskiya komin lullubewar da aka yi mata, muka kuma gane qarya komin kwalliyar da aka yi mata.

17 Sept 2016

SANARWA!!!

SALAM

Zawiyar Maulana SHEIKH SHAREEF IBRAHIM SALEH ALHUSAINY dake Zaria.

na Sanar da yan'uwa cewa ta Kammala shirye shiryen fara karatun (AL'ALIMIYYAH),a makarantar ta ta JILUL JADEED.

kuma an ware gurbane na full scholarship (Wanda ya qunshi wajen zama da karatu da abinci da kula da lafiya) guda biyar, za a yi jarabawa nan kusa domin tantance wadanda za a dauka.

16 Sept 2016

KARATUN NAHAJUL HAMEED FI MA YAJIBU ALAL MUKADDAMI WAL MURID

Insha ALLAH zamu fara karatun littafin

"An - nahajul Hameed fi ma yajibu alal muqaddami wal murid"
( KYAKKYAWAR HANYAR SANIN WAJIBIN MUQADDAMI DA MURIDI )
 na 
SHEIKH SHARIF IBRAHIM SALEH AL-HUSAINI ( CON ) 
Shugaban Kwamitin Bayar da Fatawa Karkashin Majalisar Koli ta Addinin Musulunci A Tarayyar Najeriya